Mam's Clothes Nation

Mam's Clothes Nation Sannan muna koyar da sana'o'in hannun kala kala Note: iya Mata zallah banda maza

Muna bada sarin kaya kala kala kamarsu
Dogayen riguna,Handbag, Abaya, Baby Hijabs, Zannuwan gado, Throw pillows, Baby set, Mayafai, Takalma,Yan kanti maza/mata, hulana. Zaki koyi sana'ar hannu cikin sauki kina gida batare da kinje ko me naba, munada classes guda hudu...

� MAM'S ONLINE INTERIOR AND DECOR TRAINING CLASS��

� MAM'S ONLINE TAILORING TRAINING CLASS��

� MAM'S ONLINE CHEMICALS TRAININ

G CLASS���

� MAM'S ONLINE BABY CROCHET TRAINING CLASS��

Duk zaki koyesune akan kudi kalilan, Mata a tashi a koyi sana'a Dan rufawa kai asiri da dogaro dakai.

Ina Mommys din Babygirls wannan customized summer outfit din naku domin yaranku masu capacity 👌🤩 how do you look it!   S...
29/04/2026

Ina Mommys din Babygirls wannan customized summer outfit din naku domin yaranku masu capacity 👌🤩 how do you look it! Shin bai birgeku ba!

Har kullum dai burin Mam's Clothes Nation ku fito fess daku da yaranku🥰

Always your outlook is my concern 😊🥰

Other account
Maryam Abdullahi Muhammad 🥰

Ga wasu shawara mai amfani ga masu koyan sana’ar dinki, musamman idan kina son ki zama kwararriya:Ki dage da koyo a hank...
28/04/2026

Ga wasu shawara mai amfani ga masu koyan sana’ar dinki, musamman idan kina son ki zama kwararriya:

Ki dage da koyo a hankali
Kada ki yi gaggawa. Ki koyi mataki-mataki tun daga yadda ake aunawa, yanka kaya, da dinki mai kyau. Kwarewa tana zuwa ne da lokaci.

Kuma ki cire wannan tsoron tare da ganin wani abu zai baki wahalar koya, kisa a ranki komai Mai sauki ne ta haka komai zai zo Miki cikin sauki 👌

Sannan ki sani fa, bazaki kware da dinki a kayan wani ba sai naki, dole sai kin cire tsoron zaki bata kayanki, koda zaki bata ba matsala bane tunda naki ne, tun kinayin kuskure watarana zakiyi dai dai har wasu su gani suyi sha'awa su kawo miki dinki, to indai kinsan kina koyan dinki dole ki rage Kai dinki kayanki ,kananun zannuwa ki dinga practice akai, idan Kuma kina da yarinya mace itama ki rage bada dinkinta ki dinga yi da kanki,

Indai kikabi wannan shawarar Dana Baki dandanan zaki iya dinki ki zama kwararriya, Nima Mam's Clothes Nation ta haka na kware a fannonin duk da s**a shafi dinki

Other account
Maryam Abdullahi Muhammad 🥰

Always your outlook is my concern 😊

28/04/2026

Ya kika hango babygirl dinki a cikin wannan luxury summer outfit din so Masha Allah ☺️🥰 kaya masu capacity domin Yara masu capacity 👌



🌸 Shin kin shirya fitowa da kyanki?🌸😃Kina neman kayan kwalliya masu kyau da daraja? Toh Hajiya ta maza ki garzayo Mam's ...
25/04/2026

🌸 Shin kin shirya fitowa da kyanki?🌸😃

Kina neman kayan kwalliya masu kyau da daraja? Toh Hajiya ta maza ki garzayo Mam's Clothes Nation
Burinmu ki zama ta daban, Kuma ki haskaka🤩

Har ila yau dai MAM'S CLOTHES NATION na kawo muku👇
✨ Abaya masu salo na zamani
✨ Masu kyau da inganci
✨ Sun dace da biki, suna da sha'anin yau da kullum
✨ Muna yinsu kala daban-daban
💫 “kan farashi Mai rahusa 👌

📍 Ki yi oda yanzu!
Location Jos
Nationwide delivery 🚘 cikin aminci da ikon Allah 🥰

📱 WhatsApp: 08104553098

📲 Follow us:
TikTok | Instagram | Facebook
Mam's Clothes Nation

Other account
Maryam Abdullahi Muhammad

Always your outlook is my concern 😊

🌞✨ SUMMER OUTFITS NA JARIRAI YA ISO! 👶💛Mam's Clothes Nation Na kawo muku Sabbin kaya masu laushi da dadin sakawa domin j...
23/04/2026

🌞✨ SUMMER OUTFITS NA JARIRAI YA ISO! 👶💛
Mam's Clothes Nation Na kawo muku Sabbin kaya masu laushi da dadin sakawa domin jariranku a wannan lokacin zafi! 🌿

✔️ Cotton mai dadin sakawa
✔️ Kyawawan launuka masu daukar ido
✔️ Sauƙin sawa da cirewa
🍼 Daga: 0–12 months
🎨 Launuka iri-iri akwai

💫 Ki ba jaririyarki kulawa da kyau da kwanciyar hankali a lokacin zafi!

📍 Mam's Clothes Nation
📲 WhatsApp: 08104553098
🚚 Delivery ko’ina Nationwide

Kuzo ku Saka order yanzu 🔥

Ga Yadda ake flower  rigar da kukayi requesting  step by step Bayani Yana jikin hotunanFatima Goni Ibrahim Nana M Kabir ...
21/04/2026

Ga Yadda ake flower rigar da kukayi requesting step by step Bayani Yana jikin hotunan

Fatima Goni Ibrahim
Nana M Kabir
Aisha Bashir

Ga final result na GLITTER VEIL dinmu na last week, How do you look it? So Masha Allah ☺️ wannan Gyale mai capacity ne s...
19/04/2026

Ga final result na GLITTER VEIL dinmu na last week, How do you look it? So Masha Allah ☺️ wannan Gyale mai capacity ne sai macen da tasan kwalliya ta amasa sunanta Mai Capacity👌 🤓 Indai gayu k**eso da keda yaranki kikazo Mam's Clothes Nation zance ya Kara😉

Ya kukaga Glitter veil din nan shin ya kayatar ???

Always your outlook is my concern 😊
Maryam Abdullahi Muhammad 🥰

Gamai bukatar ganin yadda nayi wannan veil din Kai tsaye kuje TikTok page dina "Mam's Clothes Nation" na daura video

Alhamdulillah 🥰 Alhamdulillah 🥰🥰 Alhamdulillah 🥰🥰🥰 Ina Godiya ga Allah da irin baiwar da ya bani, Kuma ya ciremin kyashi...
18/04/2026

Alhamdulillah 🥰 Alhamdulillah 🥰🥰 Alhamdulillah 🥰🥰🥰

Ina Godiya ga Allah da irin baiwar da ya bani, Kuma ya ciremin kyashi da hassada ta hanyar budawa wasu abinda Allah ya bani Suma su amfana kuma alhamdulillah burina Yana cika, A kullum sai na samu Wanda ya nemi Dan yamin addua da masu kirana da masu yimin DM dan kawai ayimin addua hakan na sani farin ciki Kuma Yana karamin karfin gwiwa na cigaba abinda nakeyi, masu yimin addua Ina gdy a gareku matuka👏

Masu sha'awar koyan duk wani abu da ya shafi dinki da sauran sana'oin hannu namu na mata kuje YouTube channel dina Mai suna

"Mam's Diy "
https://www.youtube.com/

TikTok
Mam's Clothes Nation
tiktok.com/

Instagram
Mam's Clothes Nation
https://www.instagram.com/mams_clothes_nation?igsh=YzljYTk1ODg3Zg==

Sannan zaku iya kasancewa dani a wannan page din nawa Mam's Clothes Nation ko account dina duk anan Facebook Maryam Abdullahi Muhammad , insha Allah zaku karu dani, burina mata su daina zaman banza a daure a koyi sana'a komai kankantarsa watarana idan akayi hakuri aka jure zai zama babba.

Always your outlook is my concern 😊

Mam's Clothes Nation komai da ruwanka kenan🤩 4 years kenan da yinsu, inason duk wani abu da ya shafi ado🥳 shiyasa ta ban...
17/04/2026

Mam's Clothes Nation komai da ruwanka kenan🤩 4 years kenan da yinsu, inason duk wani abu da ya shafi ado🥳 shiyasa ta bangaren HOME INTERIOR DECOR ba a barni a baya ba 🤓
Shin ya kukaga Throw pillows din nan sun birgeku 🤨

Always your outlook is my concern 😊
Maryam Abdullahi Muhammad 🥰

Na kwana biyu ban dira akan atamfa ba😇 yau dai Mam's Clothes Nation Nayi kaca kaca da atamfa✂️ 😖 Ina fatan dai na kokart...
16/04/2026

Na kwana biyu ban dira akan atamfa ba😇 yau dai Mam's Clothes Nation Nayi kaca kaca da atamfa✂️ 😖 Ina fatan dai na kokarta🤓

SHAWARA  A GAREKU YAN UWANA MATA MASU SANA'AR DINKI WADAN DA SUKE TASOWA Assalamu'alaikum barkanku da wannan lokacin,  Y...
14/04/2026

SHAWARA A GAREKU YAN UWANA MATA MASU SANA'AR DINKI WADAN DA SUKE TASOWA
Assalamu'alaikum barkanku da wannan lokacin, Yau Mam's Clothes Nation inada dan tsokaci akan yan uwana mata masu sana'ar dinki, akwai wadan da suke kukan ce basuda jari, ni a tunanina matsawar kika mallaki Keken dinki to kin mallaki jari, Shawarata karki ki zauna kice sai kin Jira jari sannan kiyi sana'arki, kiyi amfani da abinda k**e dashi ki jajirce Kuma kiyi hakuri, matsawar kikayi hkn da sannu nasara zata zo miki. Ni lokacin dana fara sana'ar Dinki, a cikin sana'ar na samu jari dan lokacin ban fara da abinda ya wuce 2k ba, amma ni a lokacin nayi amfani da social media wajen tallata sana'ata, idan nayi Riga daya ta Yara zan dauka a hoto na na tallata tun ba a tayawa Kuma Hakan bai sa na Karaya na daina ba, na cigaba da tallatawa har hankalin mutane yazo Kai aka fara tayawa, duk Wanda yace yana so bayan ya fadamin adadin da yake so zan sanar da mutum sai ka bani Rabin kudin kaya idan na gama aiki ka cikamin ka karbi kaya, Alhamdulillah 🥰 a haka na tafi da tsarina Kuma Allah ya dafamin Kuma har yanzu a wannan tsarin nake, Dan haka Ina kara Baku shawara ku jajirce kuyi hakuri, sannan ku tafi da zamani ta hanyar amfani da social media Dan a wannan zamanin Social media na taka mahimmiyar rawa wajen kasuwanci.
Allah ya cigaba da saka mana albarka a cikin sana'armu 🤲

Always your outlook is my concern 😊
Maryam Abdullahi Muhammad 🥰

TSAWON WANI LOKACI YA DAUKE KI KAFIN KI KOYI DINKI???Na koyi dinki a kasa da wata guda, na fara da koyan zanin gado a sa...
12/04/2026

TSAWON WANI LOKACI YA DAUKE KI KAFIN KI KOYI DINKI???

Na koyi dinki a kasa da wata guda, na fara da koyan zanin gado a satin dana fara koya naga ai zanin gado ba abu bane Mai wuya a wajena, sai na canza ra'ayi 😃 naji fah ni dinkin atamfa nakeson koya sai na juya dinkin atamfa 🤓 sati na daya da fara koyar dinkin atamfa aka fara bani bani hada kaya, Hmmm Ina yin sati uku sai na sallami kaina 😖 tun daga wannan lokacin ba Kuma komawa koyan dinki ba, saina cigaba dagwagwarmaya ta, Dan ni inada naci 🤨 da juriya akan abinda nakeso har sai na cimma burina, duk abinda na gani a hoto kawaii to saina gwada shi kuma cikin ikon Allah sai nayishi perfect 👌 Ta haka na iya kowani bangare na dinki, abu indai dinkasa akeyi sai dai idan bai fado hannun Mam's Clothes Nation 🤩 sai nayi mishi kaca kaca more especially kayan Yara, inajin nishadi a duk lokacin da nake yinsu😂

Dan haka Ina bawa duk wata Mai koyan dinki shawara ki Saka a ranki ba abu bane Mai wuya kiyi naci ki jajirce kiyi hakuri kuma, wlh indai kinyi haka ba abinda zai gagareki amma inda zaku Saka tsoro a rankaiko kisa aranki abinda k**e koya da wuya to ba shakka zai wahalar dake.
Allah dai ya cigaba da saka mana albarka a cikin sana'armu 🤲🤲

Always your outlook is my concern 😊
Maryam Abdullahi Muhammad 🥰

Address

Dorayi Babba
Kano

Telephone

+2348104553098

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mam's Clothes Nation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mam's Clothes Nation:

Share