04/03/2026
Yau da na ga yanda kowa yake rubuta buƙatarsa, sai naji wani nauyi a zuciyata… 🥺
Masu neman miji nagari sun fi yawa.
Masu neman haihuwa ma suna da yawa.
Sai na tuna cewa dukkan mu masu buƙata ne a gaban Allah 🤲🏽
Ya Allah, Ka san buƙatun kowannenmu waɗanda muka faɗa da waɗanda ba mu faɗa ba.
Masu neman miji nagari, Ka basu wanda zai zama alkhairi a duniya da lahira.
Masu neman haihuwa, Ya Allah Ka faranta musu zuciya da zuri’a ta gari.
Duk wanda ke da wata buƙata, Ya Rahman Ka biya masa ita cikin sauƙi da rahama.
Ameen Ya Rabb 🤍